Ministan Shari’a ya rubutawa Buhari wasika kan dokar zabe

Abubakar Malami with Muhammadu Buhari
Abubakar Malami with Muhammadu Buhari

Antoni Janar na kasa kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika, yana mai shaida masa matsalolin dake tattare da sabuwar dokar zabe wadda ake jiran shugaban kasa ya sanyawa hannu.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Buhari ya karbi takardar makonni 2 da suka wuce.

Mai Magana da yawun shugaban kasa Buhari ya tabbatarwa da manema labarai cewa wasikar ta isa wajen shugaban kasa, sai dai bai bayyana abubuwan da wasikar ta kunsa ba.

Sai dai wata majiya daga ma’aikatar Shari’a ta bayyana cewa wasikar ta bayyanawa shugaban kasa cewa tabbatar da dokar yin zaben fitar da gwani na kai tsaye zai iya kawo rudani a tsakanin jam’iyyu.

Wata majiyar kuma ta tabbatar da cewa wasikar ta mayar da hankali ne wajen bayyanawa shugaban kasa matsalolin dake tattare da gudanar da zaben fitar da gwani na kai tsaye.

Sai dai majiya ta ce a cikin wasikar Abubakar Malami bai ayyana sashen kundin tsarin mulkin Nigeria da ya haramta yi.

Abubakar Malami ya kuma bayyana illar dake akwai na tilastawa jam’iyyu gudanar da zaben na kai tsaye, wanda hakan zai sanya ko wace jam’iyya ta canza kundin tsarin mulkinta.

Ko da aka tuntubi mai Magana da yawun ministan shari’a Dr. Umar Gwandu ya ce bashi da damar yin Magana akan wannan batun.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here