Ministan kudi ya mikawa shugaba Tinubu mafi karancin albashin ma’aikata

Wale, Edun, Tinubu, Ministan, kudi, mikawa, shugaba, Tinubu, mafi, karancin, albashin, ma'aikata
Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya gabatar da hasashen da ake yi na kashe kudi wajen aiwatar da sabon mafi karancin albashi na kasa...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya gabatar da hasashen da ake yi na kashe kudi wajen aiwatar da sabon mafi karancin albashi na kasa ga Shugaba Bola Tinubu.

Edun tare da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Atiku Bagudu, sun gabatar wa shugaban kasa Tinubu abubuwan da suka shafi sabon mafi karancin albashin ma’aikata a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Da yake magana da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban kasar, Edun ya tabbatar da batun kuma ya tabbatar da cewa “babu wani abin fargaba.”

Karin labari: Ana ci gaba da gudanar da shari’a kan masarautar Kano

Gabatarwar da Edun ya yi na kashe-kashen ya biyo bayan wa’adin sa’o’i 48 da Shugaba Tinubu ya ba shi a ranar Talata yayin ganawarsa da tawagar gwamnati kan sabon mafi karancin albashi da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya jagoranta.

Sauran ‘yan tawagar da suka halarci taron sun hada da ministocin kudi da kasafin kudi da tsare-tsare na kasa da na kwadago dana yada labarai, da kuma babban manajan daraktan kungiyar da babban jami’in gudanarwa na kamfanin man fetur na Najeriya Limited.

Karin labari: Tinubu zai kashe Tiriliyan biyar kan tallafin man fetur

Idan dai za a iya tunawa, kungiyoyin kwadagon da suka hada da kungiyar kwadago ta Najeriya da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, sun shiga yajin aikin a fadin kasar a ranar Litinin din da ta gabata, domin neman a karawa ma’aikata albashi, tare da sauya farashin wutar lantarki da aka yi a baya-bayan nan.

Sai dai shugabannin kungiyar kwadago sun dakatar da yajin aikin ne a ranar Talatar da ta gabata na tsawon kwanaki biyar bayan da suka rattaba hannu da gwamnatin tarayya kan batun dawo da tattaunawa tare da fitar da sabon mafi karancin albashi a cikin mako guda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here