Majalisar dattawan Najeriya ta amince kafa kwamitin kudi na CBN

Majalisar, Dattawa, najeriya, kwamiti, kudi, CBN
Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin mutane 12 karkashin jagorancin gwamnan babban bankin kasar, Olayemi Cardoso a matsayin mambobin kwamitin da...

Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin mutane 12 karkashin jagorancin gwamnan babban bankin kasar, Olayemi Cardoso a matsayin mambobin kwamitin da za su kula da harkokin kudi a babban bankin Kasar CBN.

Wannan tabbacin ya zo ne bayan wani rahoton kwamitin kula da harkokin banki da inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi na babban bankin ya gabatar a zaman majalisar da aka yi ranar Alhamis.

Tabbatar da sabbin mambobin MPC ɗin na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin taron tsare-tsaren babban bankin na farko karkashin sabon gwamnan bankin.

An tsara taron ne a ranakun 26 da 27 ga watan Fabrairun 2024, mambobin su ne:

1. Olayemi Cardoso – Shugaba

2. Muhammad Sani Abdullahi – Mamba

3. Bala M. Bello – Mamba

4. Emem Usoro – Mamba

5. Philip Ikeazor – Mamba

6. Lamido Yuguda – Mamba

7. Jafiya Lydia Shehu – Mamba

8. Murtala Sabo Sagagi – Mamba

9. Aloysius Uche Ordu – Mamba

10. Aku Pauline Odinkemelu – Mamba

11. Mustapha Akinwumi – Mamba

12. Bandele A.G. Amoo – Mamba

A watan Nuwambar 2023, Cardoso wanda shugaba Tinubu ya naɗa a matsayin gwamnan CBN a watan Satumba na 2023, ya ce taron na MPC bai yi tasiri a karkashin magabacinsa Godwin Emefiele ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here