Majalisar dattijai ta amince da wani kudirin doka da ke neman a kafa asusun tallafawa masu yi wa kasa hidima NYSC.
Ƙudurin dokar wanda Sanata Yemi Adaramodu ne ya dauki nauyinsa na neman samar da dorewar samun kuɗi ga hukumar ta NYSC da koyon sana’o’i da horaswa da kuma karfafawa ‘yan kungiyar kwarin gwiwa da sake horar da ma’aikatan hukumar da kuma bunƙasa sansani mai inganci.
Karin labari: An bude shagon barasa na farko a Saudiyya
Adaramodu yayin da yake zantawa da manema labarai bayan zartar da ƙudurin dokar ya tabbatar da cewa idan aka sanya hannu kan dokar, ba za’a ci zarafin hukumar ta NYSC ba kamar sauran shirye-shiryen shiga tsakani da ake yi.