Maimakon kashe Naira biliyan 2.5 domin Auren Zawarawa, kamata ya yi a duba abinda al’umma suka fi buƙata – Martanin kungiya ga gwamnati

Mass Wedding 750x430

Kungiyar nan mai rajin yaƙi da rashin gaskiya ta “War Against Injustice” (WAI) ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta ba da fifiko ga sassa masu muhimmanci kamar ilimi, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi maimakon ware Naira biliyan 2.5 domin gudanar da bukukuwan auren Zawarawa a shekarar 2025.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta aike wa SolaceBase a ranar Litinin, babban daraktanta Kwamared Umar Ibrahim Umar, ya bayyana damuwarsa kan matakin da gwamnati ta dauka, yana mai bayyana hakan a matsayin karkatar da abubuwan da suka sa a gaba a daidai lokacin da jihar ke fama da rashin aikin yi, rashin ababen more rayuwa, da kuma tabarbarewar zamantakewa.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta ware naira biliyan 2.5 don gudanar da bukukuwan aure a cikin kasafin shekarar 2025.

Idan za a iya tunawa a shekarar 2023 sama da Naira miliyan 800 gwamnatin jihar ta kashe wajen bikin auren Zawarawa.

Kungiyar ta jaddada bukatar samar da dabarun rage kalubalen rashin aikin yi ga matasa, wanda hakan ya taimaka wajen yawaitar aikta laifuffukan a tituna kamar kwacen waya da tashe-tashen hankula na fadan daba.

Kungiyar ya ba da shawarar cewa tallafawa kananun masana’antu a yankuna kamar Bompai, Challawa, da Sharada zai karfafa ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi mai dorewa.

Hakazalika, kungiyar ta yi nuni da kalubalen da ke fuskantar bangaren kiwon lafiya, inda yawancin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ba su da isassun kayan aiki, kayan aiki, da ma’aikata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here