Kungiyoyin matasa a jihar Ogun sun bukaci Tinubu ya bude boda

Kungiyoyi, Boda, matasa, jihar, Ogun, tinubu, bude, bukaci
Gamayyar kungiyoyin matasan jihar Ogun sun yi kira ga shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu da ya bude dukkanin iyakokin kasa a wani mataki na magance matsalar...

Gamayyar kungiyoyin matasan jihar Ogun sun yi kira ga shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu da ya bude dukkanin iyakokin kasa a wani mataki na magance matsalar tsadar abinci da yadda za’a kara habaka tattalin arziki da kasar.

Karin labari: “Na dauki laifin tsanani da tsadar rayuwa da ‘yan kasa ke ciki” – Tinubu

Kakakin kungiyar Fẹmi Owoẹye, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a Abeokuta, ya roki Tinubu da ya tashi tsaye wajen shawo kan matsalar ta hanyar bude iyakokin kasa domin bunkasa tattalin arziki da rage tsadar kayan abinci.

Matasan sun kuma nuna damuwarsu kan cewa duk matakan da gwamnatin kasar ta bijiro don magance wahalhalun da ake fama da su ba su shafi matasan Najeriya ba, musamman ma wadanda ba su da aikin yi, kamar yadda Jaridar DCL Hausa ta wallafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here