Kudin da NNPC ke kashewa a tallafin mai ya wuce ƙima – Hamid Ali

6f63c4e9 7e1b 47f2 88ba 44bbb76951a8
6f63c4e9 7e1b 47f2 88ba 44bbb76951a8

Shugaban Hukumar fasa Kauri ta Najeria wato Kwastam, Kanal Hameed Ali mai ritaya, ya ce Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC, ba zai iya kare matakin yawan makudan kudaden da yake kashewa na tallafin mai a kowacce ranba ba, inda hakan ya janyo ana ɓatar na sama da naira biliyan shida a duk shekara.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Hamidu Ali ya faɗi hakan ne a ranar Alhamis, a gaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke sauraren bayani kan tsarin kashe kudi daga shekarar 2023 zuwa 2025 na matsakaicin zango.

Ya kara da cewa babu yadda NNPC zai yi bayanin ikirarin ana amfani da lita miliyan 98 a kowacce rana, inda ya yi zargin kamfanin na kara lita miliyan 38 kan ainahin wanda ake amfani da shi a kowacce ranar.

Kwamitin ya buƙaci shugaban hukumar kwastam din da ya yi bayani kan gibin da aka samu na tsakanin naira tiriliyan 11 zuwa 12 na kasafin badi.

Gwamnatin Najeriyar dai ta shigar da bukatar kasafin kudin shekara mai zuwa da ya kai naira biliyan 19.76, kuma za a samu gibin tsakanin sama da biliyan 11 zuwa sama da biliyan 12.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here