Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta bayar da umarnin wucin gadi na hana hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziƙin kasa zagon ƙasa EFCC kamawa ko musguna wa wani ɗan kasuwa ɗan Najeriya mazaunin Dubai, Alhaji Rabiu Auwalu Tijjani, wanda hukumar ta bayyana cewa ta na nemansa bisa zargin karkatar da kudi Dala miliyan 1 da dubu 900.
Wanda ya shigar da ƙarar shi ne Alhaji Rabiu Auwalu Tijjani, kuma waɗanda ake ƙara su biyu sun haɗa da EFCC da Mista Ifeanyi Ezeokoli.
Umarnin, wanda mai shari’a H. Buhari ya bayar a ranar Litinin, ya kasance martani ne ga wani ƙuduri da lauyan mai ƙara ya shigar a ranar 16 ga watan Yulin bana na neman kare haƙƙin Alhaji Tijjani na ‘yanci da walwala kamar yadda yake ƙunshe a sashe na 35 da 46 na kundin tsarin mulki na shekarar 1999.
Mai shari’a Buhari, bayan ya duba bukatar, ya bayar da umarnin wucin gadi da ya hana hukumar EFCC gayyata kamawa tsarewa ko cin zarafi, ko kuma gurfanar da Alhaji Tijjani gabanin sauraron ƙarar da kuma tantance ƙwararan hujjoji.
Kotun, ta ɗage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 18 ga Satumban shekarar nan da muke ciki ta 2025.
A baya SolaceBase ta ruwaito cewa, Hukumar Yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati EFCC ta bayyana neman Rabi’u Auwalu Tijjani bisa zargin karkatar da kuɗaɗe da suka haɗa da Dala Miliyan 1 da dubu 931 da dari 700 da ɗigo12.
Sanarwar ta fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dele Oyewale, shugaban yada labarai na EFCC, mai kwanan watan 11 ga Yuli, 2025.
Takardar shaidar ta bayyana cewa Tijjani ya kulla hulɗar kasuwanci da Mista Ifeanyi Ezeokoli a watan Janairun shekarar 2022, inda ya haɗa da musayar Dala miliyan 76 a Dubai.
Bayan cinikin, Tijjani ya ce, ya mayar wa Mista Ezeokoli fiye da Naira miliyan 26 ne bayan ya daidaita alkalumma.
Sai dai daga baya ya gano cewa shi da kansa ya biya wa Mista Ezeokoli fiye da Dala miliyan biyu saboda ya biya.
Tijjani ya kai rahoton lamarin ga hukumar tsaro ta DSS, bayan yunƙurin da aka yi na ganin an sasanta asusu da Ifeanyi ya ci tura.
Bayan haka, ɓangarorin biyu sun amince da wani bincike mai zaman kansa, wanda ake zargin ya bayyana adreshin ƙarya na kamfanonin da ke da alaka da kuɗaɗen da aka yi sama da faɗi.
Rahotonni sun ce an kwashe watanni shida ana tantancewar saboda yawan takardun hulɗa da aka yi.
Takardar shaidar ta ce Mista Ezeokoli, ya nuna rashin haɗin kai a lokacin binciken, inda a maimakon haka ya shigar da ƙara a ofishin hukumar EFCC na shiyyar Kaduna, wanda Tijjani ya yi zargin an yi ne domin a boye tafka magudi da kuma gujewa binciken hukumar DSS.













































