Kotu ta ci tarar gwamnatin Kano naira miliyan 10 kan take hakkin Aminu Ado Bayero

Rikicin, Masarautar, Kano, Aminu, Ado, Bayero, umarci, Kotu, tarar, gwamnatin, Kano, naira, miliyan
Babbar kotu da ke zamanta a Kano ta umarci gwamnatin jihar ta biya Alhaji Aminu Ado Bayero diyyar Naira miliyan 10 saboda tauye hakkinsa...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Babbar kotu da ke zamanta a Kano ta umarci gwamnatin jihar ta biya Alhaji Aminu Ado Bayero diyyar Naira miliyan 10 saboda tauye hakkinsa.

Wannan na zuwa ne bayan da mai shari’a Liman Mohammed ya bayyana cewa Alhaji Aminu Ado Bayero na da hurumin a saurari kararsa bayan ƙarar da ɗaya daga cikin masu naɗa sarki, Aminu Babba Dan-Agundi ya shigar game da rikicin masarautar Kano.

Alƙalin kotun, mai shari’a S. A. Amobeda ya ce matakin da jihar da jami’an tsaro suka ɗauka ya take hakkin walwalar Aminu Ado.

Karin labari: Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta dukkan hawan Sallah Babba

Lauyan mai kare Aminu, Mamman Lawan Yusufari, ya ce umarnin da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar na kama Aminu Ado Bayero ba tare da madogara a shari’a ba, cin zarafinsa ne da take masa haƙƙi.

Mai shari’a Amobeda ya yanke hukuncin cewa umarnin da gwamnan ya bayar barazana ce kai tsaye ga ƴancin sarkin, kamar yadda yake a sashe na 35 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kotun ta kuma tabbatar da cewa, tsarewar da aka yi wa Aminu Ado Bayero a gida ya saɓa wa hakkinsa na walwala, kamar yadda yake a sashe na 41 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Karin labari: “Za’a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta” – Tinubu

Hukuncin da kotun ta yanke ya haɗa da hana waɗanda ake ƙara ci gaba da tsare Aminu Ado ko musguna masa.

Gwamnatin Kano ta samar da dokar masarautar Kano ta 2024, tare da soke dokar masarautun Kano ta 2019, inda a dalilin haka aka sauke Aminu Ado daga kan mulki, sai dai ana ci gaba da shari’a a kotu kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here