Kano tana da masu ɗauke da cutar HIV 42,000 yayin da hukumar KSACA ke nuna damuwa kan karancin zuwa yin gwaji

WhatsApp Image 2025 12 05 at 21.54.46

Daraktan hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta Jihar Kano (KSACA), Dr. Usman Bashir, ya bayyana cewa jihar na da marasa lafiya kimanin 42,000 da aka tabbatar suna dauke da cutar HIV, wadanda ke samun magani kyauta a cibiyoyi 43 na lafiya da ke bayar da cikakken kulawa.

Dr. Bashir ya bayyana haka a wata hira da jaridar Solacebase a karshen mako, inda ya gargadi cewa yawan masu dauke da cutar HIV a Kano na iya zama mafi girma fiye da adadin da aka rubuta saboda karancin gwaje-gwaje a fadin jihar da kasa baki daya.

Ya ce, Najeriya bata kai ga cikar burin duniya na 95-95-95 ba – wato dabarar da ke bukatar kashi 95 cikin 100 na masu dauke da HIV su san matsayin lafiyarsu, kashi 95 cikin 100 daga cikin wadanda aka gano su, su samu magani mai dorewa, sannan kashi 95 cikin 100 na masu magani su samu ragin yaduwar kwayar cutar.

A baya, ayyukan yaki da HIV a Kano sun fi samun kudi daga abokan hulda na kasa da kasa sama da kashi 80%, wanda ya sa jihar dogara sosai kan tallafi na waje.

Dr. Bashir ya yaba da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan sakin Naira miliyan 300 a shekarar 2024 domin sayen kayan gwajin HIV ga mata masu ciki da sauran jama’a.

Hukumar na gudanar da gwaje-gwaje a wurare 592 da suka hada cibiyoyi na gwamnati, masu zaman kansu, da na addini, duk suna bayar da gwajin HIV kyauta.

A matsayin wani bangare na ayyukan ranar yaƙi da cutar HIV AIDs ta Duniya a 2024, KSACA ta gudanar da babban aikin wayar da kai a gidan gyaran hali na Kano, inda aka gwada fursunoni kan cutukan HIV, ciwon Hanta, Tarin fuka, da sauran su.

Karanta: Hukumar kula da lafiya da kai ɗaukin gaggawa NEMSAS ta faɗaɗa ayyukan ta zuwa jihohi 30 — Mahukunta

Haka kuma, hukumar za ta shirya wani shiri na musamman tare da masu nakasa domin tsara manufofi da suka dace da bukatunsu, musamman wadanda ke dauke da cutar HIV.

Game da sabon dokar gwajin lafiya kafin aure a Kano, wanda ke bukatar gwajin HIV, Hanta, Sikila kafin aure, Dr. Bashir ya ce ba a fara aiwatar da dokar sosai ba, amma jama’a suna bada hadin kai.

KSACA ta gudanar da zaman wayar da kai tare da limaman masallatai na Jumu’a da fastoci, wadanda suka amince cewa ba za a yi auren ba, ba tare da takardar shaidar lafiya ba.

Dr. Bashir ya nuna damuwa kan karuwar yaduwar HIV tsakanin matasa, yana mai cewa rashin wayar da kai da halaye masu hadari na daga cikin manyan abubuwan da ke kara yaduwar cutar.

Hukumar na tsara shirye-shirye na musamman don matasa domin karfafa matakan rigakafi da isar da ingantaccen bayani kan yadda HIV ke yaduwa da hanyoyin kariya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here