Jami’an hukumar EFCC sun yi dirar mikiya a gidan Rochas Okorocha

Rochas Okorocha New 640x381 1
Rochas Okorocha New 640x381 1

A yau Talata ne hukumar yaƙi da masu da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati ta EFCC ta mamaye gidan tsohon Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya ruwaito.

Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawar sun kai farmaki gidan tsohon gwamnan da ke unguwar Maitama a babban birnin tarayya Abuja domin kama shi.

A cewar gidan talabijin ɗin na Channels ya ruwaito cewa an ga jami’an EFCC a wani faifan bidiyo da suna gudanar da aiki a harabar gudan tsohon gwamnan.

Sun dage cewa Okorocha wanda ke neman tsayawa takarar shugaban kasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC ya miƙa kansa domin kama shi ko kuma ya karrama wata gayyata da hukumar ta yi masa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here