Hukumar Nimet ta yi gargaɗi kan ɓullar cutar sanƙarau a Najeriya

d9009479 f421 4972 b036 1604d4a054a6.jpg

Hukumar kula da yanayi ta kasa Nimet ta yi gargaɗin cewa wasu jihohin arewacin ƙasar na ƙara fuskantar barazanar ɓarkewar cutar sanƙarau.

Nimet a cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, ta ce jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Bauchi da Yobe da Gombe da kuma Borno su ne suka fi fuskantar barazanar.

Hukumar ta kuma ce alamomin cutar sanƙarau sun haɗa da zazzaɓi mai zafi da ciwon kai mai tsanani da riƙewar wuya da amai, sai rashin son kallon haske da ruɗewa da kuma ƙuraje.

Karanta: Hukumar NYSC ta sanar da sabuwar ranar da za ta fara biyan alawus na Naira dubu 77

Nimet ta kuma ƙara da cewa ana iya kamuwa da cutar da hanyar mu’amula da masu ɗauke da cutar da kuma shiga cunkoso, inda ta buƙaci alumma su yi rigakafi su wanke hannu su kuma gujewa kusantar masu cutar su kuma rufe bakinsu da hanci.

Hukumar ta kuma yi kira ga alumma da su yi gaggawan zuwa asibiti idan sun ji alamomin da aka bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here