Hukumar INEC ta yi hasashen mutane miliyan 90 ne za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2023

Pic. 10. INEC quarterly consultative meeting with political parties in Abuja
Pic. 10. INEC quarterly consultative meeting with political parties in Abuja
Hukumar  shirya zaɓe Mai zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ce tana kyautata zaton a ƙalla ƴan Nijeriya miliyan 90 za su kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen kasa mai zuwa na 2023.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara ofishin hafsan sojin saman Najeriya IO Amao a Abuja babban birnin kasar.

Shugaban hukumar zaben ya nemi taimakon rundunar sojan saman Najeriya wajen ganin an isar da kayan zaɓe a ƙananan hukumomi a lokaci guda lokacin zabe.

Yakubu yace aiki da rundunar shine mafita wajen kare yiwuwar samun tsaiko wajen isar da kayayyakin zabe musamman a yayin da hukumar ke kokarin ganin tayi zaben gwamna a jihar Ekiti akalla nan da makwanni biyu masu zuwa.

Ya jaddada muhimmancin kai kayayyakin zabe a runfunan zabe 190,000 lokacin zaben ‘yan majalisu a duk fadin kasar, wanda ake bukatar ganin anyi zabe a lokaci guda wato daga karfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na yamma.

Yayin jawabinsa hafsan sojin saman Nijeriya, Amao yace rundunar a shirye take don ganin ta taimakawa hukumar ta INEC wajen gudanar da ayyukan zabe ba tare da wata matsala ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here