Hukumar FAAN ta sake bude titin jirgin sama bayan hatsarin jirgin Dana

FAAN, Dana, jirgin, saman, titi
Hukumar FAAN ta sanar da jama’a da masu ruwa da tsaki cewa an sake bude titin jirgin sama mai lamba 18L/36R domin gudanar da aikin jirgin da misalin karfe...

Hukumar FAAN ta sanar da jama’a da masu ruwa da tsaki cewa an sake bude titin jirgin sama mai lamba 18L/36R domin gudanar da aikin jirgin da misalin karfe 8.00 na dare.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Misis Obiageli Orah, Daraktan Hulda da Jama’a na FAAN a ranar Talata a Legas.

Karin labari: Bidiyon yadda jirgin saman Dana ya yi hatsari a Legas

Orah ya ce lamarin ya biyo bayan rufe titin saukar jiragen da aka yi a safiyar ranar Talata, sakamakon wani lamari da ya faru da wani jirgin saman Dana Air mai lamba 5N-BKI, wanda ya mamaye titin jirgin a lokacin saukarsa.

Ta ce cikin gaggawar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta FAAN ta dauki matakin kwashe tare da kwato jirgin daga wurin.

Daga baya, an gudanar da ayyukan share fage don tabbatar da titin jirgin ba shi da ɓata kowane tarkacen abun waje (FOD) wanda zai iya hana amincin jirgin.

Karin labari: EFCC ta kama Sirika bisa zargin almundahanar naira biliyan 8 na jirgin saman Nigeria Air

Ta kara da cewa, sashen ayyuka na FAAN da hukumar NAMA, sun gudanar da cikakken bincike a kan titin jirgin tare da tabbatar da cewa ba za a iya dawo da aiki ba.

Har ila yau, an bayar da sanarwar da ta dace ga Airmen (NOTAM) game da wannan.

Hukumar ta yaba wa kowa bisa ci gaba da goyon baya da fahimtar da suke bayarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here