Gwamna Yusuf ya yi alkawarin warware duk bashin ƴan fansho da garatutin ma’aikata kafin 2027

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin biyan dukkan bashin kudaden fansho da na garatutin ma’aikata da suke binsu a jihar kafin karewar wa’adinsa na farko a shekarar 2027.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Kano yayin kaddamar da biyan kashi na biyar na Naira biliyan 5 da aka ware domin fansho da kudaden gadon ma’aikata.

Yusuf ya ce bashin da ya gada daga gwamnatocin baya ya kai Naira biliyan 48, inda ya kara da cewa gwamnatinsa ta riga ta fara biyan su a matakai.

A cewarsa, an tsara shiri na musamman domin tabbatar da biyan Naira biliyan 48 kafin 2027, kuma zuwa yanzu an riga an biya Naira biliyan 27, kuma nan ba da jimawa ba za a fara kashi na shida da na bakwai.

Gwamnan ya jaddada cewa wannan mataki na cikin kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen dawo da mutuncin tsofaffin ma’aikata da kuma rage radadin da iyalan wadanda suka rasu suke fuskanta.

Karanta: Tsofaffin Ƴan sanda na shirin yin zanga-zanga saboda matsalar Fansho

Ya kuma bukaci hakuri da fahimta daga wajen masu ritaya, tare da tabbatar musu da gaskiya da adalci a tsarin rarraba kudaden.

Shugaban Kungiyar Tsofaffin Ma’aikata ta Kasa (NUP), Godwin Abumisi, ya yaba wa gwamnan bisa wannan kuduri, inda ya yi kira gare shi da ya ci gaba da jajircewa, domin a cewarsa, da dama daga cikin masu ritaya sun riga sun mutu suna jiran hakkokinsu.

Shugaban Hukumar Kula da Asusun Fansho ta Kano, Alhaji Habu Fagge, ya bayyana cewa hukumar ta gaji bashin Naira biliyan 48 daga gwamnatocin baya, amma wannan gwamnati ta riga ta biya Naira biliyan 27.

Haka kuma, Sarkin Rano, Muhammad Umar, ya jinjinawa gwamnan bisa wannan kokari, tare da tabbatar da cewa zai amfani masu ritaya da daukacin al’ummar Kano.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar biyan kudaden, Malam Abubakar Musa, ya nuna farin cikinsa, yana mai cewa wannan taimako zai rage musu radadin rayuwa.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here