Da Dumi-Dumi: Mutane 2 sun jikkata a harin Bam a jihar Borno

Bom, jikkata, harin, jihar, borno
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da mutane 2 sun samu raunuka a ranar Lahadin da ta gabata yayin da wani harin kunar bakin wake ya sake komawa...

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da mutane 2 sun samu raunuka a ranar Lahadin da ta gabata yayin da wani harin kunar bakin wake ya sake komawa jihar.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta hannun ASP Daso Nahum, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ta ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Biu ta jihar.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar Lahadi, a lokacin da musulmin ke gudanar da sallar dare.

Karin labari: ‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya a Bauchi

“Mutumin dan kunar bakin wake wanda ake zargin zai nufi masallacin ne ya tayar da bam din da ke kusa da zagayen, inda ya kashe kansa.

“An garzaya da wasu mutane biyu da ke wucewa da bam din da suka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani.

“Nan da nan aka tura tawagar jami’an tsaron hadin gwiwa zuwa wurin da lamarin ya faru domin dawo da zaman lafiya,” inji shi.

Karin labari: ‘Yan bindiga sun kashe farar hula fiye da 100 a gabashin Burkina Faso

Rundunar ‘yan sandan ta bukaci jama’a da su kara taka tsan-tsan musamman a wannan lokaci na watan Ramadan da akasarin musulmi ke gudanar da sallar dare.

“Ya kamata mutane su tabbatar sun taka tsantsan kuma kada su yi kasa a gwiwa wajen kai rahoton duk wani yunkuri da ake da su ga jami’an tsaro,” inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here