Da Dumi-Dumi: Gwamnan Kano ya umarci jami’an tsaro su kama masu zanga-zanga

Abba, Kabir, Yusuf, rano, gaya, bichi, karaye, kano, jami'an, tsaro, kama, masu, zanga-zanga
A ranar Laraba ne Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci jami'an tsaro su kama duk wanda ya fito zanga-zanga a titunan jihar domin dakile...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

A ranar Laraba ne Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci jami’an tsaro su kama duk wanda ya fito zanga-zanga a titunan jihar domin dakile rikicin da ke neman tashi kan dambarwar masarautar Kano.

Hakan ya biyo bayan rushe masarautu 4 da gwamnatin jihar tayi da suka hada da Gaya, Bichi, Rano, da kuma Karaye, tare da cire tsohon sarki Aminu Ado Bayero daga masarautar Kano da maye gurbin shi da Muhammadu Sanusi II.

Sai dai tun bayan dambarwar, an dai hangi wasu daga cikin matasa a tituna daban-daban na jihar na nuna rashin jindadinsu ta hanyar zanga-zangar lumana.

Karin labari: HOTO: ‘Yan majalisar dokokin Kano sun kai ziyarar hadin kai ga tsohon sarki Aminu Ado Bayero

Wasu na goyon bayan Muhammad Sanusi II, wasu kuma na goyon bayan Aminu Ado Bayero.

Bayan kiraye-kiraye da aka samu daga masana da kuma hukumomi, hakan tasa gwamnan ya umarci jami’an tsaro da su kama duk masu aikata zanga-zangar don kawowa jihar Kano zaman lafiya kamar yadda jaridar DCL Hausa ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here