Da ɗumi-ɗumi: Rundunar ƴan sanda ta dakatar da hawan Sallah a Kano

Kano Durban

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta duk wasu ayyuka na hawan sallah yayin bukukuwan Sallah karama na shekarar 2025, sakamakon matsalolin tsaro da kuma bukatar tabbatar da zaman lafiya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da dakatarwar a yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda a Bompai ranar Juma’a.

Bakori ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokutan bukukuwan, domin kuwa rahotanni sun nuna yadda ake fuskantar karuwar tashe-tashen hankula da kuma barazanar da ke tattare da yin yawan sallar wanda zai iya haifar da tarzoma.

“Bayan sahihin rahotannin sirri na tsare-tsare da wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu suka shirya na yin amfani da hawan wajen kawo cikas, rundunar yan sandan tare da tuntubar gwamnatin Jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, ta yanke shawarar haramta duk wani abu na hawan sallar a fadin jihar,” in ji Bakori.

Karanta: Sallah: Dalilan da suka sa sarkin Kano na 15 Aminu Ado ya soke hawan sallah

Har ila yau, kwamishinan ya shawarci masu ibada da su gudanar da Sallar Idin da suka saba yi a wuraren da aka kebe na Sallar Idi, kamar yadda aka saba yi a baya, domin an kammala aikin samar da isasshen tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Ya yi nuni da cewa, ana gargadin jama’a da su nisanta kansu daga duk wani aiki ko hali da ka iya haifar da tarwatsa zaman lafiya ko tabarbarewar doka da oda yayin bikin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here