Manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC sun isa titin Miller a Kano, gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin shirye-shiryen sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar a hukumance a yau.
Daga cikin mutanen da suka halarta akwai tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa David Mark, sakataren jam’iyyar na ƙasa Rauf Aregbesola, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan jihar Sokoto Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

Sauran su ne Sanata Dino Melaye, da tsohon shugaban APC na ƙasa John Odigie-Oyegun, da kuma tsohon gwamnan jihar Imo Emeka Ihedioha.

Rahotanni sun nuna cewa an tarbi wannan tawaga a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano inda tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Aminu Abdussalam Gwarzo ya karɓe su.

Zuwan wadannan manyan ‘yan siyasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin sauya sheƙar Kwankwaso zuwa jam’iyyar ADC, lamarin da ke jan hankalin masu bibiyar harkokin siyasa a fadin kasar.

Sai dai ana ganin wannan sauyin sheƙa na iya zama muhimmin lamari a siyasar Najeriya, musamman duba da tasirin da Kwankwaso ke da shi a arewa da ma kasa baki daya.

Karin bayani na nan tafe…..












































