CBN Ya umarci bankuna da su dakatar da cajin kudaden ajiya

CBN, bankuna, umarci, dakatar, cajin, cirar, kudade, ajiya
Babban bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa 30 ga watan Satumba, 2024. Babban bankin ya bayyana hakan ne a wata takarda mai dauke...

Babban bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa 30 ga watan Satumba, 2024.

Babban bankin ya bayyana hakan ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 6, ga watan Mayu 2024, wanda Adetona Adedeji, daraktan kula da harkokin banki na CBN ya sa hannu.

A ranar 1 ga watan Mayu, bankuna sun dawo da tattara kudaden sarrafawa a kan ajiyar kuɗi.

Karin labari: Dalilin da yasa Gwamnan Kano ya cire shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar

A bisa umarnin, kashi 2 cikin 100 za a caje su a kan adibas sama da Naira 500,000 ga daidaikun mutane, yayin da masu asusun ajiyar kamfanoni za a caje kashi 3 bisa 100 na ajiya sama da N3,000,000.

A bisa sabon takardar da aka bai wa cibiyoyin hada-hadar kudi da kuma cibiyoyin da ba na kudi ba, CBN ya ce an dakatar da kudaden sarrafa su.

Babban bankin na CBN ya umarci cibiyoyin hada-hadar kudi da su ci gaba da karbar duk wasu kudade daga jama’a ba tare da wani caji ba har zuwa karshen kwata na uku.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here