CBN na sayar da Dala 10,000 ga kowacce BDC kan Naira 1,251/$1

Naira, Dala, CBN, BDC, sayar, karyata
Sabanin rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta na Facebook da X (Twitter) da ke ikirarin cewa ana musayar Dalar Amurka tsakanin Naira 900 zuwa...

Babban bankin Najeriya CBN,  ya fitar da wata sanarwa ga ma’aikatan ofishin BDC da ke sanar da su cewa an sayar da dala 10,000 ga kowane BDC a kan kudi Naira 1,251/$1.

Hakan na kunshe ne a wata takardar da aka rabawa manema labarai kuma daraktan sashen kasuwanci da musayar kudi na bankin, Dakta Hassan Mahmud, ya sanyawa hannu a ranar Litinin.

Karin labari: NBA ta taya Awomolo murnar zama shugaban kungiyar Benchers

Babban bankin ya umarci kowane BDC da ya sayar da dalar ga abokan cinikin da suka cancanta a kan farashin da bai wuce kashi 1.5 cikin dari ba akan farashin saye, wanda hakan ke nuna cewa ba a sa ran kowane BDC ya sayar da sama da Naira 1,269/$1.

Idan dai za a iya tunawa, babban bankin na CBN ya bayyana kudirinsa na sayar da kudaden kasar waje da darajarsu ta kai dala 20,000 ga kowane ma’aikacin da ya cancanci a yi masa canjin kudi a fadin kasar nan a watan Fabrairu.

Karin labari: Majalisar dokokin Kano ta rushe shugabannin hukumar daukar ma’aikata

Wannan dai na zuwa ne sama da shekaru biyu bayan da tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele, ya dakatar da siyar da kudaden kasashen waje ga kamfanonin BDC a wannan bangaren na kasuwar hada-hadar kudi.

Takardar ta karanta, “Muna komawa zuwa wasiƙarmu zuwa gare ku mai suna TED/DIR/CON/GOM/001/071 dangane da batun da ke sama inda CBN ta amince da kashi na biyu na siyar da FX ga BDC masu cancanta.

Karin labari: Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da belin jarumar Tik-tok Murja Kunya

“Mun rubuta ne domin sanar da ku cewa an sayar da dala 10,000 ga kowace BDC akan kudi Naira 1,251/$1.

BDCs za su sayar wa masu amfani na ƙarshe a kan yaduwar da bai wuce 1.5 bisa ɗari sama da farashin siyan ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here