Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da belin jarumar Tik-tok Murja Kunya

Murja Kunya, kotu, beli, jarumar, tik-tok
A ranar Litinin ne kotu ta bayar da belin jarumar Tik-tok Murja Ibrahim Kunya, tare da haramta mata amfani da soshiyal midiya...

A ranar Litinin ne kotu ta bayar da belin jarumar Tik-tok Murja Ibrahim Kunya, tare da haramta mata amfani da kafafen sada zumunta.

Hakan ya biyo bayan zaman kotun inda alƙalin ya ba da belin ta a kan Naira 500,000 da kuma sharuɗɗan haramta mata amfani da kowane shafin sada zumunta har zuwa lokacin kammala shari’a.

Baba Jibo Ibrahim, mai magana da yawun kotunan Kano ya tabbatar da wannan labarin, inda ya ce kotun ta ba da belin Murja ne bayan zaman kotun da aka yi a yau Litinin.

Karin labari: ‘Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar ƙarin mutum 3 a jihar Bauchi

Alƙalin ya ce dole ne ɗaya daga cikin masu tsaya mata ya zama ɗan’uwanta na jini, sannan ɗayan kuma dole ne ya zama yana da shaidar mallakar fili a Kano.

Alƙali Nasiru Saminu ya kuma ce ya bayar da belinta ne bisa hujjar cewa matashiyar ‘yar Tiktok din ta wuce kwana 30 a garƙame.

Sai dai alƙalin ya haramta wa jarumar tiktok ɗin amfani da shafukan sada zumunta har zuwa lokacin kammala shari’ar.

Karin labari: Mutum 3 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Nairobi

Alƙalin ya kuma ce kwamishinan ƴan sanda na da ikon sake kama Murja matuƙar ta ƙi mutunta umarnin haramta mata amfani da shafukan sada zumuntar tare da gabatar da ita gaban kotu.

Mai shari’ar ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Mayu don ci gaba da zama a kan shari’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here