BDC sun karyata sayar da Dala daga 900 zuwa Naira 1,000

Naira, Dala, CBN, BDC, sayar, karyata
Sabanin rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta na Facebook da X (Twitter) da ke ikirarin cewa ana musayar Dalar Amurka tsakanin Naira 900 zuwa...

Sabanin rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta na Facebook da X (Twitter) da ke ikirarin cewa ana musayar Dalar Amurka tsakanin Naira 900 zuwa 1,000 a Abuja ranar Laraba, masu gudanar da ayyukan BDC sun karyata ikirarin a matsayin labaran kanzon kurege.

An yi ta yada hotuna a shafukan Facebook da X cewa ana sayar da Dala kan Naira 1,000 a hedikwatar gundumar Wuse Zone 4 na kasuwar canjin kudade a Abuja.

Karin labari: “Zamfara a yanzu ita ce babbar wajen ta’addanci” – Gwamna Lawal

Fayil din na bogi ya ce, “A safiyar yau, a Zone 4 Abuja daura da Otal din Sheraton, ana sayar da dala kan Naira 1,000 – $1, haka kuma Abdulsalam BDC yana sayar da Naira 900 idan ya sayi sama da $5,000.

“Akwai wuce gona da iri na gaggawar zubar da daloli a Zone 4. A halin yanzu ana sayar da dala a kasuwa a kan farashi mai rahusa fiye da na kasuwa.”

Karin labari: “Tinubu ya san manyan Najeriya da ke hada kai da ‘yan bindiga” – Matthew Kukah

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta yin tsokaci a sassan rubuce-rubucen suna yin izgili ga masu yin hasashe, inda suka ce za su fuskanci illar tara Dala idan aka yi la’akari da darajar Naira a kan kudin kasashen waje a kan Naira 1,000/$1.

Sai dai a ranar Laraba da yamma a lokacin da ‘yan jarida suka ziyarci cibiyar kasuwar parallel Market da ke Wuse Zone 4 a Abuja, lamarin ya kasance sabanin haka.

Karin labari: Gobara ta lalata motoci 8 da rumfuna a jihar Kano

An sanar da su cewa an sayar da dala 1 kan Naira 1,352 a lokacin ziyarar.

“Ko CBN da NAFEX ba sa sayar da Naira 900. Adadin CBN ga BDC a safiyar yau ya kai Naira 1,251/$1,” in ji daya daga cikin ma’aikatan BDC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here