Basaraken gargajiya na Filato da aka sace ya shaki iskar ‘yanci – Soja

365AB8D2 15D5 491B 9E4C 4CEC1717275A
365AB8D2 15D5 491B 9E4C 4CEC1717275A

Da Gyang Balak, Hakimin Vwang, a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato, wanda wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi, ya samu ‘yanci daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

Maj. Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na Operation Safe Haven (OPSH) rundunar wanzar da zaman lafiya a Filato da kewaye, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Jos.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya tuna cewa a daren Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Balak a kan hanyar Jos-Vom.

Takwa ya ce nan take da aka samu labarin faruwar lamarin, kwamandan rundunar, Maj.-Gen. Ibrahim Ali, ya tura dakarun Sector 6 da ke Riyom don fara bin diddigin wadanda suka aikata laifin.

“Saboda haka, sojojin tare da sauran jami’an tsaro, gungun ‘yan banga da mafarauta, sun gudanar da aikin share fage a yankin tsaunukan Sabon Gida-Kanal, Gero da Dahol gaba daya.

“An kama mutane biyu da ake zargi a wani gidan da aka yashe a yayin aikin.”

“Wannan ci gaban ya haifar da sakin babban mai mulki a hannun wadanda suka yi garkuwa da shi kuma an hada shi da iyalansa,” in ji Takwa.

Ya ce kwamandan ya yabawa sojojin bisa kokarin da suke yi, ya kuma bukace su da su ci gaba da kara kaimi wajen yiwa kasarsu hidima.

Takwa ya kara da cewa, kwamandan ya kuma shawarci mazauna jihar ta Filato da su tallafa wa jami’an tsaro a yunkurinsu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here