Babban Limamin ya rasu yana da shekaru 130, ya bar jikoki 200, jikokin jikoki 290

0DBCBABC 9D77 4234 B227 D2B69C3EF321
0DBCBABC 9D77 4234 B227 D2B69C3EF321

Babban Limamin Masallacin Kafanchan dake Jihar Kaduna, Sheikh Adam Tahir, ya rasu yana da shekaru 130 a duniya, ya bar ‘ya’ya 26, jikokin jikoki 290 da jikoki sama da 200.

Mataimakin babban limamin Kafanchan, Alhaji Muhammad Kassim, ya ce Sheikh Adam ya rasu ne a yammacin Larabar da ta gabata sakamakon rashin lafiya.

Kassim ya ce, Musulmi zasu yi matukar kewar Marigayi Imam duba da yadda ya rayu cikin aminci, inda ya kasance abin koyi ga kowa da kowa.

A cikin sakon ta’aziyya mai martaba Sarkin Jema’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II, ya bayyana rasuwar limamin a matsayin babban rashi ga masarautar da al’ummar kudancin jihar Kaduna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here