An kashe gobarar da ta tashi a matatar man fetur ta Dangote

Matatar, Mai, Dangote, man, fetur, kashe, gobara, tashi
Shugabannin kamfanin matatar man fetur na Dangote sun ce matatar na ci gaba da aiki yadda ya kamata bayan wata gobara da ta kama a yau Laraba. A cikin wata...

Shugabannin kamfanin matatar man fetur na Dangote sun ce matatar na ci gaba da aiki yadda ya kamata bayan wata gobara da ta kama a yau Laraba.

A cikin wata sanarwa da matatar ta fitar, wadda ta wallafa a shafinta na X, wacce ta samu sa hannun mai magana da yawun matatar, Anthony Chiejina ta ce “Mun samu nasarar kashe wata ƴar gobara da ta tashi a kamfaninmu a yau Laraba 26 ga watan Yuni.

Karin labari: “Majalisar dattijai ba ta amince a sayi sabbin jirage ga shugaba Tinubu ba” – Akpabio

“Babu wata damuwa domin matatar man fetur ɗin na ci gaba da tafiyar da lamuranta sannan kuma babu wanda ya samu rauni” in ji sanarwar.

Matatar Mai Ta Dangote

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here