A ci gaba da amfani da tsofin kudi har illa masha Allah-Kotun koli

Old and New Naira Notes 750x430
Old and New Naira Notes 750x430

Kotun kolin Najeriya ta bada umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira 1000 har illa masha Allah.

Kotun kolin ta yanke hukuncin cewa a ci gaba da amfani da tsofaffi da sabbin takardun kudin har sai Gwamnatin Tarayya ta tsara yadda za’a sake fasalinsu bayan ta yi shawarwari da masu ruwa da tsaki.

Kotun mai alkalai bakwai karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro ta yanke hukuncin ne biyo bayan bukatar da gwamnatin tarayya ta gabatar na neman kotu ta kara wa’adin tsaffin kudaden domin ci gaba da amfani da su a matsayin halastattu.

Gwamnatin tarayyar ta kuma roki kotun da ta dage dokar da ta sanya tun a ranar 3 ga watan Maris tare da bayyana cewa kara wa’adin ya zama dole domin ba za ta iya buga adadin sabbin takardun da za su ba da damar kawar da tsofin kafin ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here