Da ɗumi-ɗumi: Jam’iyyar NNPP ce ke kan gaba da sama da ƙuri’u dubu 61,000 a zaben gwamnan Kano.

BREAKING
BREAKING

Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabiru Yusuf a halin yanzu yana kan gaba akan abokin hamayyarsa Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC da tazarar kuri’u sama da dubu 60,000.

Daga sakamakon da Solacebase ta tattaro a cibiyar tattara sakamakon zaben jihar, Abba Kabir ya samu kuri’u dubu 832 da 690 yayin da Nasir Gawuna na jam’iyyar APC mai mulki ya samu kuri’u dubu 771 da 333, inda aka samu tazarar kuri’u dubu 61 da 357.

SHARHI 1

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here