Kamfanin rarraba hasken lantarki na birnin Tarayya Abuja AEDC ya katse wutar gidan Gwamnatin Jihar Neja

Gov. Sani Bello
Gov. Sani Bello

Kamfanin rarraba wutar Lantarki na Abuja, AEDC, ya katse wutar ma’aikatu da hukumomin Jihar Neja, kan bashin kudaden wutar da ba a biya ba, wanda ya kai Naira biliyan 1 da miliyan 3.

Haka kuma an katse wutar sakatariyar Jihar da ta asibitoci da sauran cibiyoyin gwamnati.

Jami’in hulda da jama’a na kamfanin AEDC a Jihar Neja, Mohammed Pele, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN a Minna ranar Juma’a cewa an kuma katse wutar gidan gwamnati da asibitoci.

Pele ya Kuma bayyana cewa tun da farko sai da kamfanin ya baiwa gwamnatin jihar wa’adin mako guda domin ta biya basukan da ta tara, amma ta gaza biya.

Ya bayyana cewa, watanni hudu da suka gabata ne majalisar dokokin jihar ta shiga tsakanin kamfanin da gwamnati inda aka cimma matsaya akan cewa gwamnati ta biya kashi 80 na basussukan da kamfanin ke binta.

“Kawo yanzu babu wani alkawari daga gwamnatin jihar.

Mai magana da yawun kamfanin na AEDC, ya bayyana cewa a cikin watanni ukun da suka gabata gwamnati ta na biyan Naira miliyan 74 a duk wata na kudin da take biya, inda ya kara da cewa Naira biliyan 1 da miliyan dari 3 kudaden da ba a biya ba ne da suka taru kafin yanzu.

“Ba mu da wani zabi da ya wuce mu katse wutar sannan mu maida hankali akan abokan cinikinmu masu aminci a ciki da wajen babban birnin Tarayya Abuja.”

Pele ya yabawa masu amfani da wutar lantarkin bisa yadda suka tabbatar da biyansu kudaden wutar lantarki cikin gaggawa, ya kuma kara da cewa kamfanin ya kara taransfoma bakwai tare da kashe sama da Naira miliyan 500 don inganta wutar lantarki.

Sauran cibiyoyin gwamnatin da kamfanin ya katse musu wutar sun hada da hukumar ruwa ta jiha da makarantu da daukacin manyan asibitoci da ofishin sakataren gwamnatin jiha da na shugaban ma’aikata da dai sauransu.

A halin da ake ciki, wannan ci gaban ya haifar da tashin farashin ruwa a Minna da kashi 50 cikin 100, domin a yanzu masu sayar da ruwa suna karbar Naira 600 maimakon Naira 300 kan kurar ruwa mai jarkoki 10.

Da aka tuntubi sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Matane, ya shaida wa NAN ta wayar tarho cewa yana kan hanyarsa ta zuwa Kontagora ne domin gudanar da wani aiki a hukumance, kuma bai san da katse wutar ba.

An samu ingantuwar rarraba wutar lantarki musamman a birnin Minna cikin makonni ukun da suka gabata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here