Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da baiwa maniyyata aikin Hajji kudi Riyal 200 na Saudiyya da Ihram ga kowanne su a jihar domin aikin Hajjin shekarar 2026.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakinsa Murtala Sule Garo ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin kaddamar aikin bita a aikace da Hukumar Jin Dadin Alhazan Jihar Kano ta shirya wa maniyyata Hajji a Kano.
Da yake jawabi a wajen taron, Alhaji Murtala Sule Garo ya bayyana cewa an shirya wannan aikin ne domin wayar da kai, bayar da ilimi, da shirya maniyyatan Hajji da tsarkake musu zukata kan ayyukan Hajji tun daga Ihram zuwa Dawafi, daga Sa’i zuwa Arafat, daga Muzdalifah zuwa Mina da yadda ake jifar shaidan.
Ya bayyana cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf na ci gaba da jajircewa don jin dadin alhazan jihar baki daya.
Garo ya ce, “Wannan bita muhimmiyar gaba ce a shiri ga aikin Hajji. Hajji ba kawai tafiya ba ce ibada ce mai tsarki da ke bukatar isasshen ilimi, tarbiyya, hakuri da yin aiki da gaske ga Allah.”
Garo ya kara isar da sakon fatan alheri na Gwamna ga alhazan.
Ya kara da cewa, “Ina kuma son ba wa alhazanmu labari mai dadi cewa Gwamnatin Jihar Kano ta amince da biyan Riyal 200 na Saudiyya da Ihram ga kowane maniyyaci a matsayin kyauta daga Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf.”
Mataimakin Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta samar da wuraren zama masu dacewa domin tabbatar da jin dadin alhazan a duk tsawon zaman su a Kasa Mai Tsarki.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta kuma tura kwararrun ma’aikatan lafiya domin cike gibin ayyukan kiwon lafiya da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ke bayarwa, inda ya ce an zabi ƙwararrun malamai domin ba da jagorancin a lokacin aikin.
Ya roki maniyyatan da su zama jakadu nagari na Jihar Kano da Najeriya ta hanyar bin dokokin Saudiyya da nuna tarbiyya, tawali’u da’a a duk tsawon aikin Hajjin.











































