An ji karar wata fashewa a sararin samaniyar filin jirgin saman Dubai a ranar Asabar, tare da hango gajimaren hayaki a sama, kamar yadda wani shaida ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP, yayin da Iran ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Tekun Fasha.
Shafin bin diddigin jirage na Flightradar24 ya nuna jirage na shawagi a sararin samaniyar filin jirgin saman cikin wani yanayi da ke nuna ana jiran sauka.
Duk da hare-haren jiragen sama marasa matuka da ake kaiwa a kowace rana kan wurare a Hadaddiyar Daular Larabawa, an sake fara wasu jirage masu iyaka daga babban filin jirgin saman Dubai, wanda shi ne mafi yawan zirga-zirgar fasinjojin kasa da kasa a duniya.
Ofishin yada labaran Dubai ya bayyana a shafinsa na X cewa “wani karamin lamari ne da ya faru sakamakon faduwar wasu tarkace bayan an dakile wani hari”, tare da karyata wasu rahotannin da ke yawo game da filin jirgin.
A ranar Asabar din da ta gabata ma’aikata hudu sun ji raunuka yayin da wani bangare na ginin tashar jirgin ya lalace a filin jirgin saman Dubai, bayan barkewar yaki sakamakon hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran.
Hukumar kula da filayen jiragen saman Dubai ta ce a lokacin an shawo kan lamarin cikin gaggawa, ba tare da karin bayani ba.
Hare-haren Iran sun kuma afkawa filin jirgin saman Abu Dhabi, yankin Palm Jumeirah mai kayatarwa da kuma otal din alfarma na Burj Al Arab, yayin da tarkacen jirgin sama mara matuki ya haddasa gobara a ofishin jakadancin Amurka da ke Dubai a ranar Talata.












































