Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba ta makara ba dangane da wasikar da ta aike wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin sanya ido kan babban taronta na kasa.
Barr. Ismail Ahmed, shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa kuma mai magana da yawun kwamitin riko da tsare-tsare na musamman (CECPC) ne ya bayyana haka ranar Juma’a a Abuja yayin da yake zantawa da manema labarai.
Solacebase ta ruwaito cewa an shirya gudanar da babban taron jam’iyyar APC a ranar 26 ga watan Maris domin zaben sabbin shugabannin jam’iyyar na kasa da za su gudanar da harkokin jam’iyyar, wanda a halin yanzu CECPC ke tafiyar da shi.
Hukumar INEC a cikin wata wasika, ta yi watsi da gayyatar taron gaggawa na kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa gabanin babban taronta na kasa.
Amsar da INEC ta bayar mai kwanan ranar 9 ga watan Maris mai dauke da sa hannun Sakatariyar ta, Rose Anthony, tare da mika wa shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Hukumar ta ja hankalin jam’iyyar APC da cewa, wasikar gayyatar ba ta fito daga hannun Gwamna Mai Mala Buni, shugaban jam’iyyar APC na kasa, da Sakatarenta, Sen. John Akpanudoedehe, kamar yadda wasu dokoki suka tanada.
Ahmed, ya ce jam’iyyar APC ta bi dukkan ka’idoji kuma ta sanar da INEC yadda ya kamata.
Ya kara da cewa Farfesa Tahir Mamman, wanda ke kula da sashen shari’a na jam’iyyar zai yi magana kan lamarin nan gaba kadan.
“Za a yi babban taron jam’iyyar APC na kasa a ranar 26 ga Maris. Ni ba shugaban matasa ba ne kawai, ni ma lauya ne. Kuma mun mika wa INEC sanarwar ranar 26 ga watan Fabrairu da ta gabata.
“Mun ba da sanarwar a ranar 5 ga Fabrairu kuma wannan shine kwanaki 21 da ake buƙata.
Idan za ku yi wani gyara ga wannan ranar duk abin da kuke buƙata shine wasiƙar yin gyara ga kwanan wata.
“Ba kwa buƙatar ƙarin kwanaki 21 kuma an rubuta wasiƙar kimanin makonni biyu da suka gabata, lokacin da muka fahimci cewa ba za mu iya riƙe ta a ranar 26 ga Fabrairu ba.
Ya kara da cewa idan akwai wanda ke da matsala kan hukuncin da jam’iyyar ta dauka kan shugabancinta, zai iya zuwa kotu.
Sai dai ya yi kira ga kafafen yada labarai da su kasance masu natsuwa a cikin rahoton da suke bayarwa, kuma a ko yaushe su rika tantance bayanai kafin su buga.












































