Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wata motar kaya dauke da kwalaben giya fiye da dubu 24, da aka shiga da ita jihar.
Hukumar wadda ta kwace giyar akan hayar Zariya ta kuma kama direban motar da wasu mutum biyu.
Karanta wannan: Zargin almundahana: EFCC ta kama shugabar hukumar NSIP, Halima Shehu
Darakta Janar na hukumar Alhaji Abba Sufi, shi ne ya tabbatar da kama motar a cikin wata sanrwa da mai Magana da yawun hukumar Lawan Ibrahim Fagge ya fitar ranar Laraba a Kano.
Karanta wannan: Hukumar ICPC ta fara gudanar da bincike kan zargin kammala digiri cikin mako 6 a Benin
“Mun kwace wata motar daukar kaya makare da giya akan hanyar Zariya cikin daren ranar Talata.
“Jami’an Hisbah suna aiki ba dare ba rana don ganin an kau da badala a fadin jihar Kano.











































