Ma’aikatan Kiwon Lafiya 400,000 Basu Isa Najeriya ba-FG

Health Workers new
Health Workers new

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ya ce kusan ma’aikatan kiwon lafiya 400,000 a Najeriya ba su isa ba wajen biyan bukatun kiwon lafiyar ‘yan Najeriya.

Pate ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a Abuja, bayan taron kwanaki uku da ya yi da ma’aikatu da hukumomin da ke karkashin ma’aikatar. Ma’aikatar ta shirya taron ne domin tsara wani tsari na tsarin kiwon lafiyar Najeriya.

A cewar Pate, ma’aikatan 400,000 sun hada da ma’aikatan kiwon lafiya na al’umma, ma’aikatan jinya, ungozoma, masu hada magunguna, likitoci, masana kimiyya, masu fasaha, da mataimakan da ke aiki a tsarin kiwon lafiyar Najeriya.

“Ba su isa ba idan kuna tunanin cewa wannan adadin zai iya kula da mutane miliyan 220. Adadin likitocinmu da yawan jama’a ya yi ƙasa da abin da Hukumar Lafiya ta Duniya ke tsammani.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here