Ɗan siyasar Kano ya rasu yayin jana’izar Mahmoud Madakin Gini

WhatsApp Image 2025 06 16 at 21.08.37 750x430

Wani abun alhini ya sake aukuwa a yau Litinin a Kano yayin da tsohon shugaban karamar hukumar Wudil Abubakar Abdullahi Likita, ya faɗi ya rasu a lokacin da ake sallar jana’izar amininsa kuma na hannun damar siyasa, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dala, Mahmoud Sani Madakin Gini.

Rahotonni sun bayyana cewa marigayi Likita ya faɗi ne yayin da ake ci gaba da gudanar da Sallar Jana’izar Madakin Gini, lamarin da ya haifar da kaɗuwa da alhini ga waɗanda suka halarci jana’izar.

Ƙoƙarin ceto shi bai yi nasara ba, kuma an tabbatar da mutuwarsa ba da jimawa ba.

Wani makusancin ɗan siyasar marigayi Abubakar Musa ya tabbatar wa da Solacebase cewa za a yi jana’izar Likita gobe Talata da karfe 10:00 na safe a gidansa da ke unguwar Bompai.

Haka kuma rahotonni sun bayyana cewa marigayi Abubakar Likita ya na cikin mota daya da tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen da ya gabata na shekarar 2023 Dakta Nasir Yusuf Gawuna, wanda ya kai su sallar jana’izar Mahmood Sani Madakin Gini.

A baya Solacebase ta ruwaito cewa tsohon shugaban karamar hukumar Dala, Mahmood Sani Madakin Gini, ya rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja yau Litinin.

Mutuwar fitattun ‘yan siyasan nan guda biyu ta jefa alhini a kan yanayin siyasar Kano, musamman ma waɗanda suka yi aiki a lokacin gwamnatin Shekarau.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here