Zargin ɓata suna: Sanata Natasha ta maka Akpabio a kotu, tare da nema Naira biliyan 100.3 na shigar da ƙara 

akpabio and natasha

Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya a majalisar dattijan kasar nan Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da ƙara a kotu tana ƙalubalantar shugaban majalisar dattajai, Godswil Akpabio, kan zargin ɓata mata suna.

Natsha ta shigar da karar ne gaban babbar kotun tarayya a ranar Talata, tana mai ƙarar Akpabio da babban mai taimaka masa Mfon Patrick.

Ta nemi kotun tarayyar da ta umarci waɗanda ake karar su biya ta naira biliyan 100 kan zargin ɓata mata suna, sannan a biya ta naira miliyan 300 a matsayin kuɗin shigar da ƙara.

Akpoti, wadda lauyanta Victor Giwa ya shigar da ƙarar a madadinta, ya bayyana cewar kalaman da babban mai taimaka wa shugaban majalisar dattawan ya wallafa a shafinsa na facebook ba komai ba ne illa ɓata suna, da tsokanar fada, da ƙaskantar da ita a idon abokan aikinta, da sauran al’umma.

Sanata Natasha ta bukaci kotun da ta haramta wa waɗanda ake ƙara ko makusantansa daga wallafa duk wani rubutu na batanci a game da ita.

A makon da ya gabata ne Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta bayyana damuwarta kan yadda aka bai wa wani dan majalisa wurin zamanta, saboda wasu sauye-sauye da aka yi a tsarin zaman majalisar, Inda ta ki amincewa da sauyin wajen zaman da aka yi mata, wanda hakan ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ta da shugaban majalisar dattawan.

Tuni aka umarci kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawan da ya gayyaci Sanata Natasha don bin bahasi kan rikicin sauyin wajen zaman.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here