Za’a kai Falasɗinawa cibiyoyin jin-ƙai kafin ƙaddamar da hari a Rafah

Rafah, gaza, sake, tsagaita, wuta
Masu shiga tsakani na Isra'ila za su fara tattaunawa a Qatar, da ake fatan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a Gaza. Ɓangarorin biyu dai na fuskantar...

Sojojin Isra’ila sun ce sun shirya kai Falasɗinawan da suka rasa muhallansu a Gaza zuwa abin da suka kira cibiyoyin jin-ƙai a tsakiyar zirin gabanin ƙaddamar da ƙudurinsu na kai hari ta ƙasa.

Sun ce za ta kwashe mutanen ne daga Rafah a kudancin Gaza zuwa tsibiran sannan kuma za su ba su kayan jin ƙai da kuma muhalli na wucen gadi duk da wurin da ake shawarar kai su ya lalace sakamakon yawan hare-haren da aka kai ta sama da ƙasa.

Karin labari: “Ba za mu biya ƴan bindiga ko sisin kwabo ba” – Tinubu

Rafah dai ta cunkushe da fiye da Falasɗinawa miliyan ɗaya waɗanda hare-haren Isra’ila suka tilasta musu tserewa daga gidajensu a Gaza.

Duk da gargaɗin da ƙasashen duniya suka yi, Isra’ila ta dage cewa kai hari ta ƙasa kan birnin ne hanya tilo ta murƙushe Hamas.

Amurka ta ce dole ne Isra’ila ta nuna tana da wani tsari na kare farar hula kafin kai irin wannan hari a Rafah.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here