Za’a fara shigo da doya Najeriya daga China

Doya, shigo, china, najeriya
Gwamnatin Najeriya ta ce nan gaba kadan ‘yan kasar zasu fara shigar da doya daga China duk kuwa da cewa kasar ke da kaso 67 na yawan doyar da ake fitarwa a...

Gwamnatin Najeriya ta ce nan gaba kadan ‘yan kasar zasu fara shigar da doya daga China duk kuwa da cewa kasar ke da kaso 67 na yawan doyar da ake fitarwa a duniya.

Babban sakataren ma’aikatar noma da raya karkara Ernest Umakihe ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani a wajen taron masu ruwa da tsaki kan harkokin noma da ya gudana a birnin tarayyar Abuja.

Karin labari: Mutane 10 sun mutu tare da jikkatar mutum 48 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Ya ce a yanayin yadda China ta shiga kasuwar cinikayyar doya a duniya da karfin ta, da kuma irin tasirin da take da shi a kasuwar duniya za ta iya cika kasuwar Najeriya da doyar da take samarwa.

Ya ce wannan shi ne lokacin da ya kamata a ce ‘yan Najeriya su mayar da hankali wajen noman doya, la’akari da farin jinin da take da shi a kasashen duniya da kuma kudaden da ake samu.

Ya koka a kan  yadda wannan lamari ka iya haddasa rashin aikin yi ga dimbin matasan kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here