Yanzu-yanzu: NELFUND ta amince da bayar da lamunin ɗalibai

Dalibai, NELFUND, amince, bayar, lamunin, ɗalibai, mabuƙata
Asusun ba da lamunin ilimi na Najeriya (NELFUND) ta amince da bayar da lamunin ɗalibai ga masu bukata da nasara. NELFUND ta gudanar da taronta na farko a...

Asusun ba da lamunin ilimi na Najeriya (NELFUND) ta amince da bayar da lamunin ɗalibai ga masu bukata da nasara.

NELFUND ta gudanar da taronta na farko a ranar Larabar da ta gabata, wanda ke nuna wani gagarumin ci gaba a yunkurinta na tallafawa dalibai da tallafin kudi.

A karkashin jagorancin shugabanta Mista Jim Ovia, hukumar ta amince da bayar da lamunin dalibai ga wadanda suka yi nasara.

Karin labari: Yanzu Yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Shiga Ganawar  Sirri Da ASUU

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Laraba daga asusun X na hukumar dauke da sa hannun shugabanta, na yada labarai da hulda da jama’a, Nasir Ayitogo.

Sanarwar mai taken, “NELFUND ta gudanar da taron kwamitin farko a matsayin Babban Ajandar Rarraba Lamunin Dalibai.”

Taron wanda ya samu halartar masu kula da asusun da wakilan kungiyoyin mambobi, ya kuma aza harsashi kan shirye-shiryen da za a yi nan gaba na bunkasa damar ilimi da tallafawa dalibai a bangarori daban-daban.

Karin labari: Shugaban kasar Kenya ya janye shirin haraji bayan gudanar da zanga-zanga

Amincewa da lamunin da NELFUND ta yi na nuna wani mataki na ƙarfafa tsararraki masu zuwa ta hanyar ilimi.

Sanarwar ta ce, “Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya (NELFUND) a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni, 2024 ta gudanar da taron kaddamar da kwamitinta a Abuja.

“Taron ya nuna gagarumin ci gaba a kudurin kungiyar na karfafawa dalibai ta hanyar tallafin kudi.

Karin labari: “Majalisar dattijai ba ta amince a sayi sabbin jirage ga shugaba Tinubu ba” – Akpabio

“A karkashin jagorancin shugaban hukumar, Mista Jim Ovia, babban abin da aka tattauna shi ne amincewa da bayar da lamunin dalibai ga masu neman nasara.”

A cewar sanarwar, wannan mataki ya yi dai-dai da burin fadar shugaban kasa na inganta harkar ilimi da samar da sauki ga kowa da kowa.

“Wannan shawarar ta kara jaddada sadaukarwar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na bayar da tallafin kudi ga daliban da ke bukata a kan lokaci da muhimmanci, wanda zai ba su damar cimma burinsu na ilimi ba tare da yankewar kudi ba.

Karin labari: Kotu ta umarci a ƙwace dala miliyan 1.4 daga hannun Emefiele

Shugaba  Tinubu ya sanya hannu a ranar 3 ga watan Afrilu, 2024, kan dokar lamunin daliban.

An fara rajistar shirin ne a watan Mayu tare da dalibai miliyan 1.2 a manyan makarantun tarayya a fadin kasar wadanda suka fara zangon farko.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here