Yanzu-Yanzu: Masu Zanga-Zanga Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa

Picture of the broken gate as seen on Wednesday
Picture of the broken gate as seen on Wednesday

Masu zanga-zangar cire tallafin mai da ƙungiyoyar ƙwadago ta kasa (NLC) ke jagoranta sun ɓalle ƙofar shigar majalisar dokoki ta ƙasa.

Rahotanni sun nuna fusatattun masu zanga-zangar ta NLC da takwararta TUC sun balla kofar shiga majalisar ne bayan takaddama da jami’an tsaro da ke gadin harabar majalisar.

Sun isa wurin ne bisa jagorancin shugaban NLC Joe Ajaero da takwaransa na TUC Festus Osifo, inda suka bukaci jami’an tsaron sun bude musu domin su shiga su gabatar da korafinsu, amma jami’an tsaro suka ki.

Ana cikin haka ne ’yan kungiyar suka yi kukan kura suka karya kokar suka kutsa cikin harabar majalisar da karfin tuwo domin huce haushinsu.

Tallafin mai da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi tun a jawabinsa na bayan karbar rantsuwar fara aiki ya sa farashin fetur tahin gwauron zabo daga N197 zuwa 620.

Hakan ya haifar ta hauhawar farashin kayan masarufi da na sufuri, wanda kawo yanzu ’yan kasar ba su ga alamar sassautawarsu

Hakazalika, duk da karin farashin da aka samu na wadandannan kayayyakin bukatu na yau da kullum, har yanzu ba a yi musu karin albashi ba.

Ko da yake gwamnatin kasar ta sanar da shirinta na ba da tallafin N8,000 a duk wata na tsawon wata 6 ga masu tsananin bukata guda miliyan 12 a kasar, matakin da al’ummar kasar ke ganin mara amfani ne.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here