Yan sanda sun kashe ƴan bindiga 3 tare da kama 2 bayan sun kai hari kan ofishin INEC

police 1 750x430 1
police 1 750x430 1

Gwamna Hope Uzodimma na Imo ya ce jami’an tsaro sun kashe ƴan bindiga uku tare da kama wasu biyu bisa samun su da kai hari kan ofishin hukumar zabe ta kasa, INEC a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a shelkwatar ƴan sanda da ke Imo yayin da aka kama ‘yan bindigar da aka kashe.

A jiya Litinin ne dai wasu ‘yan bindiga su ka kai hari ofishin INEC da ke Imo, inda suka kona wani bangare na harabar ofishin da wasu motoci.

Gwamnan ya bayyana cewa jami’an tsaro a jihar suna sintiri lungu da sako na Owerri, babban birnin jihar, domin kamo ɓatagarin da suka tsere da raunukan harbin bindiga a lokacin da ‘yan sanda suka kama su a ofishin INEC.

“Muna son mu san meye manufar kai hare-hare a ofisoshin INEC. Abin da ke faruwa a jihar Imo siyasa ce kawai kuma bai kamata ba.

“INEC ba ta bukatar irin wannan karkatar da hankali a wannan lokaci da lokacin zabenmu, a’a, ya kamata kowa ya ba ta goyon baya.

“Hukumomin tsaro sun shirya, za a yi zabe a Imo da yardar Allah. Makiya jihar mu ba za su ti nasara ba,” inji shi

Da ya ke jawabi kwamishinan ‘yan sanda na Imo, Mohammed Barde, ya ce ‘yan sandan sun samu nasarar kashe uku daga cikin ‘yan bindigar tare da cafke biyu yayin da sauran suka tsere da raunukan harbin bindiga.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here