‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane 8 da ake Zargi da yiwaa ‘Yan Bindiga safarar Alburusai da babura a Zamfara

AHK 1
AHK 1

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wasu mutane 8 da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga alburusai da kakin soja da babura da kayan abinci a jihar.

An kuma ce wasu daga cikin wadanda ake zargin sun same su da laifin hada kai tare da karbar makudan kudade a matsayin kudin fansa daga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Gusau, inda yace rundunar ta kama wadanda ake zargin ne a kananan hukumomin Gusau da Tsafe.

Shehu ya ce biyar daga cikin wadanda ake zargin sun kware wajen bayar da bayanan sirri, da kuma samar da makaman soji da alburusai ga ‘yan bindigar.
“Jami’an ‘yan sanda sun yi amfani da bayanan sirri kan wani da ake zargi da aikata laifin, Zainu Lawali.

Ya ce an kama Lawali wanda ya yi ikirarin cewa shi tsohon soja ne sanye da kakin soji, da katin shaida na soja amma na bogi da harsashi hudu da wasu muggan makamai.

Ya kara da cewa daya daga cikin wadanda aka kama, Alhassan Lawali, ya amsa laifin cewa ya baiwa ‘yan fashin babura 14 akan kudi naira dubu 750,000 kowanne daya.

Shehu ya kara da cewa, ‘yan sandan da suke sintiri a kan hanyar Gusau zuwa KotorKoshi zuwa Mada, sun kama wani dan bindiga mai suna Umar Manaro da ke addabar jama’a a yankunan Mada da Kotorkoki na jihar.

Ya kara da cewa, “Yayin bincike, an gano AK-49 guda daya da harsashi mai rai guda 174 a hannunsa.”
A cewarsa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here