Yan Majalisun Dokokin Kano hudu sun yi mi’ara koma baya

Screenshot 20220525 081747
Screenshot 20220525 081747

Yanzu haka dai Dan Majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar mazabar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a zauren Majalisar, dokokin jihar Kano Hon. Kabiru Yusuf Isma’il, ya fice daga NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, a baya dai mataimakin shugaban majalisar, Zubairu Hamza Massu, mai wakiltar karamar hukumar Sumaila, ya fice daga APC, zuwa NNPP, tare da wasu takwarorin sa guda 3, cikin su akwai Abdullahi Yaryasa mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, sai kuma Muhammad Butu-butu mai wakiltar Tofa da Rimin Gado da Kuma Kabir Isma’il mai wakiltar Madobi.

Sanarwar da Kwamishinan yada labaran jihar Kano Malam Muhd Garba, ya fitar a ranar Larabar nan ya rawaito cewa Dan majalisar dake wakiltar Ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, Hon Mu’azzam El-Yakub ya fice daga NNPC zuwa APC.

Sanarwar dai ta bayyana cewa yanzu sabuwar jam’iyyar NNPP na tsaka da fuskantar matsalar shige da fice a wannan lokaci.

“Tuni dai mun san cewa wakilin kananan hukumomin Bagwai da Shanono a majalisar dokokin ya koma APC, haka takwaran sa na karamar hukumar Danbatta Hon. Murtala Kore, shi ma ya fice zuwa APC”. A cewar Muhd Garba.

Sai dai kuma masana a bangaren siyasa na ta hasashen cewa sabuwar jam’iyyar NNPP, akwai yiwuwar ta taka muhimmiyar rawa a zabe mai zuwa, musamman ganin yadda manyan jam’iyyun PDP da APC, suke daukar wasu daga cikin yayansu a matsayin Dan mowa da Dan bora.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here