‘Yan Majalisa sun soki yawan ‘yan tawagar da Buhari ya kai Amurka

ffac56e0 3a07 11ed 9ae9 959994b8a64c.jpg
ffac56e0 3a07 11ed 9ae9 959994b8a64c.jpg

Wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin Najeriya sun soki tawagar kusan mutum 100 da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta zuwa birnin New York na Amurka domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

‘Yan majalisar da ke sukar tawagar, sun ce bai kamata a haɗa dandazon jama’a kusan mutum dari ba a wannan lokaci da Najeriya take fama da matsin tattalin arziki.

A taron da ke zamar wa Buharin na karshe a matsayin shugaban kasa.

Shugaban ya yi jawabinsa na ban-kwana a wajen babban taron.

Sai dai ‘yan majalisar irin su Sanata Muhammad Sani Musa, na Majalisar Dattawa, ya ce wannan taro ne da ake yi a kowacce shekara kuma kowa ya ga irin ayarin da yake dauka wajen tafiya irin wadannan tarukan tun hawansa mulki.

Sanatan ya ce zance na gaskiya akwai rashin kyautawa da adalci, musamman a bangaren mashawarta ko mukarraban shugaban kasar da yake cewa ba sa fada masa gaskiya ko kyautata masa.

Ya ce: ”Da ake nuna tawagar a talabijin har kunya na ji, saboda ana kuka a kasa cewa babu kudi, har ana tunanin ciyo bashi domin cike gibin kasafin kudi, to ina dalilin wannan tafiya?”, a cewar sanatan.

Sanatan ya kuma ce duk waɗannan tawaga karkashin gwamnati dole a biya musu kudin tikiti da dakin kwana da abinci da kuma kudaden alawus.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here