‘Yan kasuwa a Afirka ta Kudu sun yi barazanar shigar da ƙarar gwamnati kan ƙarancin wutar lantarki

326116995 928177688190802 3691582267878269535 n
326116995 928177688190802 3691582267878269535 n

Kungiyoyin ‘yan kasuwa a Afirka ta Kudu sun yi barazanar shigar da ƙarar gwamnatin ƙasar saboda matsalar wutar lantarki da ake fuskanta a faɗin ƙasar.

Sun bai wa gwamnati daga nan zuwa ranar Juma’a domin daidaita harkokin samar da wutar lantarki ko ta fuskanci hukuncin kotu.

Kungiyoyin sun rubuta wata wasika zuwa ga ministan masana’antu Pravin Gordhan, inda suka ce hakkin gwamnati ne na samar da wutar lantarki ga jama’a.

Mutane sun yi ta fuskantar ƙarancin wutar lantarki sama da shekaru goma saboda rashin iya gudanarwa da cin hanci da rashawa.

A baya-bayan nan ma, ƙasar ta yi ta fama da ɗaukewar wutar lantarki na sama da sa’a goma a kowace rana.

Matsalar ta sanya shugaban ƙasar katse ziyarar da yaso yi a birnin Davos don tattaunawa da ‘yan kasuwa da kuma shugabannin kungiyoyin kwadago

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here