Yajin aikin ASUU: Farfesa J.D Aminu Ze jagoranci kwamitin shugabannin jami’o’i dan warware matsaolin yajin aiki

asuu 1 1
asuu 1 1

Kwamitin mataimakan shugabannin jami’o’in Najeriya ya kafa wata tawaga don samarda ingantaccen hadin kai mai dorewa domin warware rikicin da ya dabaibaye gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Tsohon Sakatare Janar na Kwamitin Farfesa Michael Faborode, kuma babban jami’i na tawagar, ya tabbatar da haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.

Ya ce burin kungiyar shi ne kar a bari tabarbarewar da ake fuskanta a tattaunawar yajin aikin ASUU ta cigaba da wakana, domin yajin aikin ya yi yawa.

A cewar sanarwar Kwamitin ya fidda jerin sunayen na ƙarshe da zasu jagorancin wannan aiki tukuru dake tafe.

Ya ce tawagar ta kunshi tsohon mataimakin shugaban jami’ar Maiduguri Farfesa Jibrilla Dahiru Aminu; se tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ibadan Emeritus Farfesa Olufemi Bamiro; Farfesa Ekanem Braide, Shugaban Kwalejin Kimiyya; da Dr Nkechi Nwagogu, tsohon Uban Jami’ar Calabar.

Sauran ‘yan tawagar su ne Farfesa Joe Ahaneku, tsohon mataimakin shugaban jami’ar Nnamdi Azikiwe; Farfesa Fatima Mukhtar, tsohuwar mataimakiyar shugabar jami’ar tarayya ta Dutse; da Farfesa Akpan Ekpo, tsohon mataimakin shugaban jami’ar Uyo.

Haka kuma a cikin tawagar akwai Farfesa Yakubu Ochefu, Babban Sakatare, Kwamitin Mataimakan Jami’o’in Najeriya da Farfesa Michael Faborode, tsohon Sakatare Janar na CVCNU kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Obafemi Awolowo.

A cewarsa, gwamnatin tarayya da kuma kungiyar ASUU, ana kokarin ganin sun amince da shiga tsakani na kungiyar dattawan kasar.

“Tawagar za ta tuntubi kwamitin Farfesa Nimi Briggs don fahimtar tushen abubuwan shawarwarin da suka bayar, kuma suyi nazari gwamnatin tarayya da ASUU don gano makasudin abubuwan da ke damun su.

Faborode ya ce kungiyar ta zayyana wasu shawarwari na farko da za su iya zama fitila dan warware dukkanin takaddamar.

Ya ce hakan ya faru ne sakamakon yawaitar dambarwar da ake samu a rikicin da ake ganin kamar yana kara ta’azzara gwamnatin tarayya ta tsaya tsayin daka na cewa babu aiki, ba biya ba, ta kuma umarci ASUU da ta koma bakin
aiki.

Ya ce wannan mataki da gwamnati ta dauka ya sanya kungiyar ASUU ta tsawaita yajin aikin ta na sai-baba- tagani domin bangarorin biyun da basa ga miciji da juna.

Daganan yayi kira ga Majalisar kasa da ta bada ta ta gudunmawar wajan samarda mafita tareda tabbatar da samarda isassun kudade don gudanar da Jami’o’in kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here