Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya mayar da Dakta Danlami Hayyo a matsayin sakataren ilimi, tare da kuma maido da Michael Ango a matsayin shugaban riƙo na Hukumar Harajin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ministan ya dakatar da Dakta Danlami Hayyo daga mukaminsa bayan wata sanarwa da ta yadu wadda ta umarci makarantun gwamnati a Abuja su rufe, lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin jama’a da hukumomin ilimi.
Sanarwar, wadda daraktar ayyukan makarantu Aishatu Sani Alhassan ta sanya wa hannu, ta umurci dukkan manyan makarantun sakandare na gwamnati a Babban Birnin Tarayya Abuja da su rufe makarantu bisa dalilan tsaro da ba a fayyace ba, tare da umartar shugabannin makarantu su dakatar da karatu su sallami ɗalibai cikin tsari da aminci.
Sai dai gwamnatin Babban Birnin Tarayya Abuja ta bayyana cewa ba ta amince da irin wannan umarni ba, tana mai cewa babu wani sahihin izini da ya bayar na rufe makarantun a wancan lokaci.
Karin labari: Wike ya yi bikin cika shekaru 58 da haihuwa, ya ce ba ya nadamar goyon bayan Tinubu
Haka kuma, ministan ya sauke Michael Ango daga mukaminsa na shugaban riƙo na Hukumar Harajin Babban Birnin Tarayya Abuja, inda a wancan lokaci ba a bayyana wani dalili a hukumance ba kan matakin da aka ɗauka.
Sanarwar maido da mutanen biyu ta fito ta bakin babbar mataimakiya ta musamman ga ministan kan sadarwa da kafafen sada zumunta, Lere Olayinka, inda ministan ya ja kunnen jami’an gwamnatin Babban Birnin Tarayya Abuja cewa ba za a lamunci rashin ladabi da karya ƙa’ida ba, tare da umartar Dakta Danlami Hayyo da Mista Michael Ango su koma bakin aiki nan take.













































