Tinubu ya nemi majalisa ƙara yawan kuɗin kasafin 2025 zuwa Tiriliyan 54.2

Bola Tinubu sabo 720x430 (1)

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi majalisa ta yi ƙari a kasafin kuɗin da ya gabatar na shekarar 2025 daga naira triliyan 49.7 zuwa naira triliyan 54.2.

Kamfanin dillancin Labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, buƙatar hakan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da shugaban ya aike wa shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, wanda ya karanta a zaman majalisar a yau Laraba.

A cikin wasiƙar, shugaban ya ce buƙatar ƙarin ta taso ne sakamakon samun ƙarin kuɗaɗen shiga na naira triliyan 1.4 daga hukumar tattara haraji ta ƙasa FIRS, da naira triliyan 1.2 daga hukumar hana-fasa-ƙwauri ta kwastam, sai kuma naira triliyan 1.8 daga wasu hukumomin gwamnati.

Bayan karanto wasiƙar, shugaban majalisar dattawan ya buƙaci kwamitin da ke kula da kasafin kuɗin kan su gaggauta duba batun.

Ya kuma tabbatar cewa za a kammala dubawa da amincewa da kasafin kudin kafin ƙarshen Fabrairu.NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here