Tinubu ya gana da hamshaƙan ‘ƴan kasuwar Najeriya

Tinubu, gana, 'yan kasuwa, najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawa da manyan ‘yan kasuwa masu zaman kansu da wasu gwamnonin jihohin ƙasar, inda suka tattauna halin da...

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawa da manyan ‘yan kasuwa masu zaman kansu da wasu gwamnonin jihohin ƙasar, inda suka tattauna halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da kuma tsadar rayuwar da ‘yan ƙasar ke fuskanta.

Taron ya kuma tattauna kan yadda darajar Naira ke faɗuwa yayin da darajar dalar Amurka ke ƙara tashi, a yayin ganawar ta ranar Lahadi.

Karin labari: Mutane 7 sun mutu a wajen sayen shinkafa a ofishin kwastan

Baya ga batun tattalin arziki taron ya kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi wadata ƙasar da abinci da kuma na tsaro.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa “kamar yadda na sha faɗa al’ummar kasar nan su ne kaɗai mu ke da su, kuma muke son kyautatawa, mun damu matuƙa da halin da suke ciki”

Karin labari: Mutum 17 Sun Rasu Wajen Rububin Kudi A Unguwar Hausawan Kalaba

Cikin waɗanda suka halarci taron a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, sun haɗa da attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote.

“Mun tattauna kan batun samar da ayyukan yi da wasu batutuwa da dama… abin alfaharin shi ne Najeriya ƙasa ce mai albarka, kuma mu na da kyakkayawan fata kan za mu iya sauya tattalin arzikinmu kuma za mu tabbatar da hakan.” In ji Dangote.

Karin labari: “Gwamnatin Najeriya ta wofintar da mu a Sudan” – Wasu Dalibai

Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ƙwadago ta NLC ke shirye-shiryen yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Miliyoyin ‘ƴan ƙasar ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci da yunwa, lamarin da ake alaƙantawa da cire tallafin mai da kuma sauran gyaran fuskar da shugaban ƙasar ya yi tun bayan hawansa mulki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here