Tinubu ya ƙaddamar da majalisar kula da tattalin arzikin Najeriya

0

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da majalisar tattalin arzikin kasa (NEC).

An kaddamar da majalisar ne ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima a zauren majalisar da safiyar ranar Alhamis.

A wani saƙo da Dada Olusegun, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa ya wallafa a shafinsa na twitter ya ce an ƙaddamar da majalisar ne a zaurenta da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja.

Ƙwarya-ƙwaryar bikin ya samu halartar shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume da gwamnonin jihohin Najeriya 36.

Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da majalisar, shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnonin su haɗa kai, wajen bunƙasa ƙananan hukumomi da ababen more rayuwa, duba da manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

“Ni da ku duk muna buƙatar hakan, kan haka muka gudanar da yakin neman zaɓukanmu, har ma muka yi rawa a gaban jama’a don jaddada alƙawuranmu, don haka, ba mu da dalilin yin korafi kan haka. ‘Yan Najeriya na nuna mana goyon baya. Suna son gyara kuma suna son hakan cikin gaggawa”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here